<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Paul Baloche, Hastings, Thomas (1784-1872), Toplady, Augustus Montague (1740-1778)</author>
<title>Yesu Mai Jin Tausayi, Ga Ni Nan A Gabanka LW178</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu mai jin tausayi, ga ni nan a gabanka.
 Ni na cika zunubi, laifina ya kā da ni.
 Babu wani Mai Ceto sai dai kai. ya Almasihu.

[V2]
 2) Kome niyyar da na yi garin zaman adali,
 Ko ƙoƙari na ke yi garin barin zunubi
 Duk ya kasa cetona, sai ka sake halina.

[V3]
 3) Ban da kuɗin fansata, ga ni nan a wurinka.
 Sai ka kau da laifina da jininka, Ɗan Allah.
 Sai ka ba ni sabon rai har in bi ka, kai kaɗai.

[V4]
 4) Cikin duniyan nan yanzu haɗa ni da cetattu.
 Kome wuya, sai in bi kusa da Ubangiji,
 Ba da ikon kaina ba, sai da ikon Ruhunka.</lyrics>
<hymn_number>178</hymn_number>
</song>